Breaking News

Babu alakar rasuwar Shema’u Sani da matsalar sabbin kudi a asibitin Nassarawa – Dr. Tsanyawa.

 

By: Mukhtar Yahaya Shehu.

Ma’aikatar lafiya ta jihar kano ta musanta zargin da wata kafar yada labarai ta yi cewa wata Mai dauke da juna biyu ta rasu a asibitin Nassarawa saboda matsalar sabbin kudi.

Kwamishinan lafiya na jihar kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai Dangane da rasuwar Shema’u Sani Labaran yayin haihuwa a asibitin Nassarawa a makon da ya gabata.

Ya ce tun bayan fitar wancan labari ma’aikatar lafiya ta jihar kano hadin guiwa da hukumar kula da manyan asibitoci ta jiha suka kafa kwamiti domin bincika lamarin.

Dr. Tsanyawa ya ce binciken da ma’aikatar lafiya ta gudanar ya gani cewa marigayiya Shema’u Sani Labaran an kawo ta asibitin bayan ta dauki tsawon sa’o’i 4 tana zubar da jini a gida kafin a kawo ta asibitin,Kuma tun bayan kawo ta asibitin Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya suka duku fa domin ceto rayuwarta.

“Tun bayan karbar marigayiya Shema’u ba a saurari komai game da biyan kudi ba, ciki Kuma har da Kara mata jini”. Dr. Tsanyawa.

Kwamishinan ya ce tun bayan umarnin gwamnatin jihar kano na kula wa da mata masu dauke da juna biyu kyauta a dukkanin asibitin gwamnati babu wata alakar rasuwar Shema’u Sani Labaran da matsalar sabbin kudi.

Idan za a tuna wa a makon da ya gabata ne wani Mai suna Malam Bello ya yi hira da wata kafar yada labarai bisa zargin rasuwar Mai dakinsa Shema’u Sani asibitin Nassarawa saboda matsalar sabbin kudi.

Leave a Comment