Breaking News

Kungiyar G7 Business Community ta kaddamar da kungiyoyi sama da dari (100) a Kano – Hon Ibrahim

By: Kabiru Getso

kungiyar yan Kasuwa ta G7 Business Community tayi gagarumin gangamin taron ganawa da kungiyoyi domin kaddamar da su da kuma wayar dakan mambobin akan sha’anin gudanar da zabe a mako mai zuwa.

Babban Daraktan kungiyar Hon Ibrahim Baba Ahmad ya bayyana cewa, zasu samar da Muliyoyin kuri’u ga jam’iyyar APC a zaben mai zuwa, domin tuni shiri yayi nisa na yin hakan.

Hon Baba ya yi jawabin hakan a babban taron da kungiyar ta hada a Babban wajen taro na (star light) dake cikin Birnin Kano, yace duba da yadda Shuwagabannin kungiyoyin al’ummar da dama suka amsa gayyatar taron ya nuna a fili cewa jam’iyyar APC zata lashe zabukan da ke tafe baki daya.

Hon Baba yace sun gaddamar da Shuwagabannin kungiyoyi sama da 100 wadanda dukkanninsu akwai dinbin al’umma a karkashinsu, kuma suma zasu je suyi aiki tukuru tare da sauran mambobinsu don ganin jam’iyyar APC ta samu gagarumin rinjaye a dukkanin zabukan dake tafe.

Hon Baba ya shawarci Mata da su guji yin kunshi da sauran abubuwa da zasu kawo cikas a lokacin kada kuri’u wanda hakan ka iya haifar da asarar kuri’un nasu, don haka wajibi ne suyi kokarin kiyaye wadannan sharuda da hukumar zaben ta bayyana.

Shima a nasa jawabin Tsohon Shugaban karamar hukumar kunbotso kuma dan takarar majalisar dokoki dom wakilcin Karamar hukumar Hon Abdulkadir Fansheka ya yabawa kungiyar ta G7 Business Community bisa irin wannan kokari da take tare da kira ga mahalarta taron da suyi duk mai yiwuwa domin ganin jam’iyyar APC ta samu gagarumin rinjaye a dukkanin zabukan dake tafe.

Taron ya samu halartar manyan mutane na ciki da wajen jihar Kano.

Leave a Comment